Ana tammahar wuta a maƙera, ta fito a masaƙa.
Recent Updates Toggle Comment Threads | Keyboard Shortcuts
-
useibert
-
useibert
Gishiri na yi wa man kaɗe dariyar rana, ran da ruwa ya zo gishiri ya ji kunya.
-
useibert
“Gandoki, mu je biki”, ta ce, “zanena ya yi gaba ko.”
-
useibert
Ba a bori da sanyin jiki.
-
useibert
Abin nema ya samu! Matar ɗan sanda ta haifi ɓarawo.
-
useibert
Babu irin daren da jemage bai gani ba.
-
useibert
Abin aljihu na mai riga ne.
-
useibert
A riƙa sara, ana duban bakin gatari.
-
useibert
Tawa ta same ni! Kura da hatsin gandu.
-
useibert
Wasa tare ci bambam?
-
useibert
A sa a baka, ya fi a rataya.
-
useibert
Kada a yi “ban ruwa albasa” a ɗiba a ƙasa, a zuba a ƙasa.
-
useibert
Takobi mai kaifi ba aminci da wargi nasa.
-
useibert
Inda wani ya mutu nan wani kan tashi.
-
useibert
Gari da gawa ba a wucewa da tufaniya.
-
useibert
Mu ji mu gani an rufe tsofuwa da rai.
-
useibert
Ko’ina funtu zashi, da sanin mai riga.
-
useibert
Tattauran kashi shi ke tare zawo.
-
useibert
Ba cas, ba as, shanyar goruba.
-
useibert
Ta’adin ƙwai sai kaza, ƙadangare sai gyaɗa kai.
-
useibert
Yaushe a gari? Kare ya ji kugin kura.
-
useibert
Abu mai sauƙi! Kura ta je gidan maharbi.
-
useibert
Yaro da gari abokin tafiyar manya.
-
useibert
Tsari mai ban haushi a kore ka ka faɗa ruwa.
-
useibert
Makafo bai san ana ganinsa ba, sai an sa sanda an zungure shi.
-
useibert
Akurkin ɗunɗu wawa ka sa hannu.
useibert 9:29 am on 12. December 2022 Permalink |
Just for fun, I have asked ChatGPT to do a translation. Here is the answer I got:
It’s difficult for me to provide an accurate translation of this Hausa phrase without more context. “Ana tammahar wuta a maƙera” could be translated as “there is a fire burning in the market,” but the exact meaning would depend on the context in which it is used. “Ta fito a masaƙa” could be translated as “it came out in the square,” but again, the meaning would depend on the context. Without more information, it’s difficult for me to provide a more accurate translation.
I added the comment: It’s a proverb. The reply from ChatGPT was:
In that case, the proverb “Ana tammahar wuta a maƙera, ta fito a masaƙa” could be translated as “The fire that burns in the market emerges in the square.” This proverb is likely intended to convey the idea that the consequences of one’s actions will eventually become known to others, even if they are hidden at first. It suggests that it is important to be careful and mindful of one’s actions, as they can have far-reaching effects.
LikeLike